Nijar za ta samu babban dauki daga Italiya

Angelino Alfano da Mohamadou IssoufouHakkin mallakar hotoANGELINO ALFONO TWITTER
Image captionAngelino Alfano ya fada wa Mohammadou Issoufou cewa Italiya na son zama abokiyar hulda da Jamhuriyar Nijar a lokaci mai tsawo

Gwamnatin Italiya ta ce za ta karkata kashi 40 cikin 100 na tallafin kudin da take ba wa kasashen Afirka zuwa Jamhuriyar Nijar.

Ministan harkokin wajen Italiya, Angelino Alfano, wanda ke ziyara a Niamey babban birnin Nijar ne ya sanar da haka bayan ya gana da Shugaba Mohamadou Issoufou.

Mista Angelino Alfano ya yi amfani da wani bangare na wannan ziyara inda ya bude ofishin jakadancin kasar Italiya na farko a yankin kasashen Sahel.

Batun tsaro dai shi ne ya kankane tattaunawar bangarorin guda biyu, inda ministan ya fada wa manema labarai cewa karfafa huldar tattalin arziki tsakanin kasashen biyu, wani bangare ne da Italiya ke bai wa fifiko.

Italiya a matsayinta na kasa ta uku mafi karfin tattalin arziki a Turai, ta kara kokarinta wajen hada gwiwa da kasashen yankin Sahel wadanda a baya ta yi biris da su.

A watan Disamba ma, Italiya ta tura sabbin dakarunta zuwa Jamhuriyar Nijar.

Haka zalika a cikin wani sakon tiwita, ministan harkokin wajen ya kuma yi tsokaci game da matsalar kwararar ‘yan ci-rani zuwa Turai da ke ratsawa ta Jamhuriyar Nijar.

Nijar na daya daga cikin kasashen yankin Sahel biyar – da suka hadar da Mali da Chadi da Burkina Faso da Mauritania wadanda suka kafa wata rundunar hadin gwiwa don yaki da barazanar ta’addanci daga kungiyoyin masu ikirarin jihadi.

A bara ma, sai da Tarayyar Turai ta amince ta ba da tallafin sama da yuro miliyan 50 ga rundunar sojin hadin gwiwar da suka fito da kasashen Mauritania da Mali da Chadi da Burkina Faso da kuma Nijar.

BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *