‘Yan bindiga sun hallaka mutum bakwai a jihar Ribas

Lamarin ya auku ne a garin Egbeda da ke yankin karamar hukumar Emohua na jihar Ribas
Image captionLamarin ya auku ne a garin Egbeda da ke yankin karamar hukumar Emohua na jihar Ribas

Wasu ‘yan bindiga sun kashe mutane akalla bakwai a wata gona a jihar Ribas da ke kudu maso gabashin Najeria.

Lamarin ya auku ne a garin Egbeda da ke yankin karamar hukumar Emohua na jihar Ribas, inda ake zargin wasu ‘yan bindiga ne suka kai harin, kuma ana tsammanin sun hallaka akalla mutum bakwai.

DSP Omoni Nnamdi, shi ne jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, kuma ya tabbatar wa da BBC faruwar lamarin.

Ya kuma kara da cewa, “Wasu samari ‘yan kungiyar asiri ne suka kai harin ramuwar gayya kan wasu abokan hamayyarsu na wata kungiyar asirin da ke kauyen, ana kuma fargabar mutane biyu sun rasa rayukansu a lokacin farmakin. Amma dai mun sami nasarar kashe wutar tashin hankalin, har ma mun damke mutane hudu daga cikin wadanda ake zargin su suka kai harin a jiya.”

  • An hallaka basaraken gargajiya da matarsa a Kaduna
  • An sace Basaraken Zangon Kataf a Kaduna

Sakataren basaraken gargajiya na garin na Egbeda Cif Francis Ebee JP ya yi karin bayani inda ya ce: “Wasu ‘yan bindiga ne kawai suka yi wa garin dirar mikiya, suka shuga harbi irin na kan mai uwa da wabi. A sakamakon haka an kashe mutane shida. Amma a zancen da nake yi da kai yanzu haka, an turo isassun ‘yan sanda da sojoji, kuma al’amuran sun fara komowa kamar yadda aka saba.”

Wannan hari da aka kai garin Egbeda dai ya auku ne kwanaki kadan, bayan wani harin da aka kai garin Omuku na jihar ta Ribas, a jajiberin shigowar sabuwar shekara aka hallaka mutane 16.

BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *