‘Kuskuren rubutu aka yi wajen nadin kwamishiniyar walwalar ma’aurata’

A watan Octoba ma Mista Okorocha ya yi ta shan suka sakamakon gina mutum-mutumin shugaba kasar Afirka ta Kudu, Jacob Zuma na tagullaHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES

Image captionA watan Octoba ma Mista Okorocha ya yi ta shan suka sakamakon gina mutum-mutumin shugaba kasar Afirka ta Kudu, Jacob Zuma na tagulla

Gwamnatin jihar Imo ta ce kuskuren keken rubutu aka yi wajen nadin kwamishiniyar walwalar ma’aurata a jihar.

A ranar Litini ne ce-ce-ku-ce ya barke a shafukan sada zumunta da muhawara a Najeriya bayan da Gwamna Rochas Okorocha ya nada kanwarsa cikin sabbin kwamishinoni 28 da aka rantsar a jihar.

Sai dai a wata sanarwa, sakataren yada labarai na gwamnan jihar Mr Sam Onwuemeodo ya ce maimakon a rubuta kwamishiniyar jin dadi da taimakawa al’umma cika burin su, sai aka rubuta kwamishiniyar jin dadi da walwalar ma’aurata.

  • Rochas na shan suka kan nada kanwarsa kwamishiniyar walwalar ma’aurata
  • Mutum-mutumin Zuma: Okorocha na shan suka

Ya kara da cewa an kirkiro da ma’aikatar don taimakawa ma’aikatun da hukomimin gwamnati kan abubuwan da suka zama wajibi su aiwatar don tabbatar da jin dadin rayuwar al’umma.

Sanarwar ta kara da cewa gwamnan ya zabi kanwarsa Misis Ogechi Ololo ce saboda kwarewarta wajen tafiyar da harkokin mulki.

Mutane da dama dai sun yi ta tafka muhawara kan nadin da Mista Okorocha ya yi wa kanwar tasa, inda da dama ke ganin babu wani abun burgewa wajen kirkiro sabon matsayin na kwamishiniyar jin dadi da walwalar ma’aurata.

Wasu kuma da dama na ganin bai kamata ya bai wa kanwar tasa Mrs. Ogechi Ololo nee Okorocha, mukamin kwamishiniya ba.

Misis Ololo dai mata ce ga wani injiniya Chuks, wanda dan majalisar wakilan tarayya ne, kuma ta rike mukamai da dama tun bayan zamowar dan uwanta gwamna a shekarar 2011, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Kafin a nada ta kwamishiniyar jin dadi da walwalar ma’aurata dai, tana rike da mukamin mataimakiyar shugaban ma’aikatan gidan gwamnati da kuma mai ba da shawara ta musamman kan al’amuran cikin gida ga gwamnan.

BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *