Israel: An yi arangama a Yammacin Kogin Jordan kan birnin Kudus

Rikici ya barke a Bethlehem

A kalla Falasdinawa 16 ne suka ji rauni a wani tashin hankali da aka yi a Yammacin Kogin Jordan, yayin da ake zanga-zangar nuna adawa da matakin da Shugaban Amurka Donald Trump ya dauka na mayar da Kudus babban birnin Isra’ila.

Rahotanni sun nuna cewa mutane sun samu raunukan ne sakamkon jefa musu hayaki mai sa hawaye da harsashin roba, amma an ji wa mutum daya rauni sakamakon harbinsa da aka yi da harsashi.

Isra’ila ta girke karin daruruwan dakaru a Yammacin Kogin Jordan.

Sanarwar da Mista Trump ya yi dai ba ta samu karbuwa ba a duniya baki daya, inda ake yin tur da hakan saboda sauya tsarin Amurka na gomman shekaru a kan wannan lamari mai sarkakiya.

Falasdinawa mazauna Yammacin Kogin Jordan da Zirin Gaza sun mamaye tituna don gudanar da zanga-zanga.

Mafi yawan abokan Amurka na kut-da-kut sun ce ba su yarda da matakin ba, kuma Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar kasashen Larabawa za su yi taro nan da kwanaki masu zuwa, don mayar da martani kan batu.

  • Kasashen duniya sun yi caa kan Trump
  • Trump ya debo ruwan dafa kansa — Hamas

Akwai fargaba cewa sanarwar za ta iya sabunta barkewar fada. Kungiyar Falasadinawa ta Hamas tuni ta yi kira da a yi zanga-zangar Intifada.

Me Trump ke cewa?

A ranar Laraba ne shugaban Amurka ya ce ya yi amanna lokaci ne ya yi na mayar da Kudus babban birnin Isra’ila.

“Na dauki wannan mataki ne don kare martabar Amurka da kuma neman kawo zaman lafiya tsakanin Yahudawa da Falasdinawa,” in ji shi.

Ya ce ya umarci ma’aikatar harkokin wajen Amurka da ta fara shirin mayar da ofishin jakadancinta Kudus daga Tel Aviv.

Duk da gargadin rashin zaman lafiya da za a iya samu a yankin, matakin ya zama cikar alkawarin da Mista Trump ya dauka ne a lokacin neman zabensa.

Ya kara da cewa: “Mayar da Kudus babban birnin Isra’ila ba wani ba ne face amincewa da abun da ya kamata a yi a zahiri.

“Kuma abu ne da ya kamata a yi.”

BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *