Atiku zai zama dan kallo ne a babban taronmu — PDP

Atiku da MakarfiHakkin mallakar hotoATIKU FACEBOOK

Babbar jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta ce tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, bai cancanci kada kuri’a ba a babban taron jam’iyyar da zai gudana ranar Asabar.

Jam’iyyar PDP dai za ta yi babban taron ta ne a Abuja don zaben shugabannin da za su ci gaba da jan ragamar jam’iyyar.

Barista Abdullahi Jalo, wanda shi ne mai bai wa shugaban jam’iyyar na riko Ahmed Makarfi, shawara kan harkokin watsa labarai na Hausa, ya shaida wa BBC cewa, karkashin dokar Jam’iyyar, sai Atiku ya kai shekara guda a cikinta kafin ya samu damar yin zabe ko kuma a zabe shi a taron jam’iyyar.

Ya kara da cewa Atiku zai iya samun damar yin zabe a babban taron ne kawai idan kwamitin zartarwa na jam’iyyar ya jingine masa dokar da ta haramta masa yin zabe wanda kuma ba a yi hakan ba kawo yanzu.

  • Atiku Abubakar ya koma PDP
  • ‘Atiku Abubakar zai kawo rigima a PDP’
  • Buhari ya kawo canjin ‘rigar mahaukaci’

Sai dai Barista Abdullah ya ce za a bai wa Atiku Abubakar damar yin jawabi ga ‘ya’yan jam’iyyar a taron domin ya zaburar da wasu da suka sauya sheka su dawo, amma ba zai yi zabe ba a taron.

Shi dai Atiku Abubakar ya fice daga jam’iyyar APC mai mulki ne tun a watan Nuwambar 2017, inda ya ce jam’iyyar “ta kasa cika alkawuran da ta yi wa al’ummar kasar musamman matasa.”

A martanin da ta mayar game da komawar Atiku cikinta, jam’iyyar PDP ta ce tsohon mataimakin shugaban kasar ya dawo gida ne, da ma bakunta ya je yi a jam’iyyar APC.

Image captionJam’iyyar PDP a Najeriya ta ce Atiku Abubakar gida ya dawo da ma bakunta ya je yi APC.
BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *