Ai Atiku gida ya dawo dama bakunta yaje — PDP

Jam'iyyar PDP a Najeriya, ta ce Atiku Abubakar, gida ya dawo dama bakunta yaje
Image captionJam’iyyar PDP a Najeriya, ta ce Atiku Abubakar, gida ya dawo dama bakunta yaje

A Najeriya, yayin da a ranar Lahadin da ta gabata ne tsohon mataimakin shugaban kasar Alhaji Atiku Abubakar, ya sanar da komawarsa babbar jam’iyyar adawa ta PDP a kasar, jam’iyyar PDP ta ce dama ai gida ya dawo.

Barista Abdullahi Jalo, wanda shi ne mai ba wa shugaban jam’iyyar na riko Ahmed Makarfi, shawara kan harkokin watsa labarai na Hausa, ya shaida wa BBC cewa, dama bakunta Atiku Abubakar din ya je jam’iyyar APC mai mulki, amma yanzu da ya ke lokaci ya yi ai ya dawo gida.

Dangane da rade-radin da ake yi cewa tsohon mataimakin shugaban Najeriyar ya koma jam’iyyar PDP ne don ya nemi takarar shugabancin kasar, Barista Jalo ya ce ” mutane na fadar hakan ne ba tare da la’akari da abinda kundin tsarin mulkin jam’iyarmu ya tanada ba da kuma matsayin da ake ciki a yanzu” .

Don haka ya ce, yakamata mutane su daina riga malam shiga masallaci a kan abinda ba su da tabbas, kuma shi Atiku Abubakar din ya fadi cewa zai tsaya takara ne? Inji Barista Jalo.

  • Ba zan bi Atiku Abubakar ba — Bindow
  • Atiku Abubakar ya fice daga jam’iyyar APC

Alhaji Atiku Abubakar, ya fice daga jam’iyyar APC mai mulki ne tun a watan jiya inda ya ce jam’iyyar APC ta “kasa cika alkawuran da ta yi wa al’ummar kasar musamman matasa.”

BBC Hausa

Don haka ya koma jam’iyyar PDP ne kuma saboda matsalolin da suka sa ya fice daga ita a shekarar 2014, an warware su yanzu.

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *