Kun san mutum nawa ne ke dauke da cutar AIDS a Nigeria?

Kimanin mutane miliyan 34 ne a duniya ke fama da cutar AIDS ko SIDA mai karya garkuwar jikiHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionKimanin mutane miliyan 34 ne a duniya ke fama da cutar AIDS ko SIDA mai karya garkuwar jiki

Ranar 1 ga watan Disambar kowace shekara, rana ce da aka kebe don hada kan al’ummar duniya da nufin yaki da cutar AIDS ko SIDA mai karya garkuwar jiki.

Haka kuma rana ce da ake nuna goyon baya ga mutanen da suka kamu da cutar tare da tunawa da wadanda ta zama ajalinsu.

Yawancin mutanen da suka kamu da cutar na bukatar magani kullum domin hana kwayar cutar HIV karya garkuwan jikinsu, lamarin da ke jawo AIDS.

Wani kiyasi na hukumomin lafiya ya ce akwai kimanin mutane miliyan 34 a duniya da ke fama da cutar.

Majalisar Dinkin Duniya dai ta ce tana rubanya samar da magani ga mutanen da ke dauke da cutar cikin shekaru biyar.

A Najeriya mutane 900,000 ne kawai ke samun damar shan magani na kashe kaifin cutarHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionA Najeriya mutane 900,000 ne kawai ke samun damar shan magani na kashe kaifin cutar

Kawo yanzu fiye da mutane miliyan 35 ne suka mutu sakamakon cutar, abin da ya sa ta zama daya daga cikin annoba mafi ta’adi a tarihi.

Wani kwararre kan harkar cutar AIDS Malam Musa Bungudu ya shaidawa BBC cewa Nigeria ce kasa ta biyu a yawan masu dauke da cutar AIDS bayan Afrika ta Kudu.

Ya ce fiye da mutum miliyan uku ne su ke dauke da cutar a Nigeria, inda Jihar Akwa- Ibom ke kan gaba wajen masu dauke da cutar.

  • ‘Rashin abinci ya sa magungunan HIV na wahalar da mu’
  • ‘Ana samun raguwar HIV/AIDS a Kaduna’
  • Rayuwar mata masu fama da cutar kanjamau. BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *