Nigeria: Za a fara rijistar jarrabawar shiga jam’ia

JAMBHakkin mallakar hotoFACEBOOK/JAMB
Image captionA yanzu dai ana rubuta jarabarawar shiga jami’ar ne ta hnayar Intanet

Shugaban hukumar JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede, ya ce hukumar za ta fara yi wa masu sha’awar shiga makarantun gaba da sakandare a 2018 rijista ranar 22 ga watan Nuwamba.

Farfesa Ishaq ya ce za a shafe wata biyu ana yi wa masu sha’awar shiga jami’o’i da kwalejojin kimiyya da fasaha da kuma kwalejojin ilimi rijista sabanin wata daya da aka yi ana rijistar a shekarar 2017.

Shugaban hukumar, wanda da ya yi jawabi a wani taron masu ruwa da tsaki a kan jarrabawar, ya ce za a yi jarrabawar ta shekara mai zuwa ne tsakanin ranar 9 zuwa 17 ga watan Maris na shekarar 2018.

  • An sayar da zanen Yesu Almasihu sama da N150b

Ya jaddada cewa hukumar a shirye take wajen ganin domin rijista tare da gudanar da jarabawar, yana mai cewa hukumar tasa za ta gudanar da ayyukanta kamar yadda jadawalin da ta fitar ya nuna.

Jarrabawar shiga jami’a da kwalejojin ilimi da kuma kwalejojin kimiyya da fasaha aba ce wadda matasa da iyaye suke sha’awar yin nasara akai domin ci gaban yara.

JAMBHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionMatasa da yawa a Najeriya suna da burin karatu a jami’a, amman gurbin karatun ya yi musu kadan.
BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *