Yadda ake musguna wa Musulmin Rohingya a Myanmar

RohingyaHakkin mallakar hotoEPA
Image captionMajalisar Dinkin Duniya ta ce ‘yan gudun hijirar Rohingya na bukatar muhalli akalla guda 60,000

Akalla Musulmai ‘yan kabilar Rohingya 290,000 daga jihar Rakhine a kasar Myanmar suka ketara zuwa kasar Bangladesh mai makwabta cikin makonni biyu da suka wuce.

Musulmin ‘yan gudun hirar na cewa sojojin Myanmar su na kona kauyukansu- zargin da sojojin ke musantawa.

Tashin hankalin ya fara ne a ranar 25 ga watan Agustan da ya gabata lokacin da wata kungiyar gwagwarmayar ‘yan Rohingya ta kai wa wani ofishin ‘yan sanda hari a arewacin jihar Rakhine.

Daga nan ne sai sojojin Myanmar suka fara murkushe su, kamar yadda ‘yan kabilar Rohingya suka bayyana.

Sai dai gwamnatin kasar ta musanta hakan, inda ta ce ta na yakar “‘yan ta’addan” Rohingya ne kawai.

  • An kama ‘babban kwamandan IS’ a Kano
  • Yadda ake cinikin ‘yan aiki a intanet

‘Yan Rohingya wadanda galibinsu Musulmi ne da ba su da kasa, na rayuwa ne a kasar Myanmar wacce mabiya addinin Buddha ke da rinjaye.

Kungiyoyin ba da agaji a Bangladesh sun ce adadin ‘yan gudun hijirar Rohingya da ke shiga kasar ya wuce wanda za su iya dauka, yayin da ake cewa akwai dubban ‘yan Rohingya da ke tsaye a gefen hanya, suna rokon abinci.

Wani wakilin kamfanin dillancin labarai na AP ya ce, ya hangi wani mutum da ya yanke jiki ya fadi yayin da yake bin layin abinci.

Har ila yau, wani wakilin BBC ya ce a kan idonsa aka cinnawa wani kauyen Musulmin Rohingya wuta a jihar Rakhine da ke Myanmar.

Ana ci gaba da yin kalaman Allah-wadai game da yadda gwamnatin Myanmar ta ke musgunawa Musulmi tsiraru ‘yan kabilar Rohingya.

Mawuyacin halin da Musulmin ke ciki ya sa ana sukar Shugabar Kasar Aung San Suu Kyi kan yadda ta ki ta kare su daga musgunawar da suke ci gaba da fuskanta.

Har yanzu babu adadin yawan Musulmi ‘yan Rohingya da suka rasa rayukansu sanadiyyar rikicin

Shugabannin kasashen duniya sun bukaci Misis Suu Kyi, wadda ta taba lashe kyautar Nobel ta Zaman Lafiya da ta fito ta yi magana a madadin ‘yan Rohingyan.

Koda yake ta amsa kiran daga bisani, inda ta ce “kafofin yada labarai na kara gishiri game da abin da yake faruwa a jihar Rakhine.”

Daga nan ta ce “ana kula da duk wani mutum da yake zaune a Myanmar dan kasa da kuma bako, muna iya kokarinmu duk da cewa ba mu da wadata sosai.”

Tarihin kabilar Rohingya

Akwai kimanin ‘yan kabilar Rohingya miliyan daya da dubu dari uku a Myanmar, yayin da kuma wadansu miliyan daya da rabi suke rayuwa a wadansu kasashen duniya galibinsu ‘yan gudun hijira ne.

Yawancinsu Musulmi ne, kodayake akwai wadansu tsiraru daga cikinsu da ke bin addinin Hindu.

Majalisar Dinkin Duniya ta taba bayyana su a matsayin al’ummar da tafi fuskantar tsangwama a fadin duniya.

A shekarar 1982 ne gwamnatin kasar Myanmar ko kuma Burma ta kirkiri wata sabuwar doka wadda ta hana wa ‘yan Rohingya damar su ta kasancewa ‘yan kasa.

Gwamntin Myanmar tana cewa su ba ‘yan kasarta ba ne, ‘yan cirani ne daga kasar Bangladesh.

Duk da cewa kabilar tana cewa ta samu asali ne tun a karni na takwas, amma gwamnatin kasar ba ta daukarta a matsayin daya daga cikin dimbin kabilun kasar.

A Myanmar an takaita wa ‘yan Rohingya damar zirga-zirga da neman ilimi da kuma damar yin aikin gwamnati, kamar yadda kungiyar kare hakkin dan Adam ta Human Rights Watch ta bayyana.

Ba bana ne karon farko da ‘yan Rohingya suke fuskantar wannan musgunawar ba.

Musulmin Rohingya sun fuskanci musgunawa daga sojojin Myanmar a shekarun 1978 da 1992 da 2012 da 2015 da 2016 da kuma 2017.

Wanne taimako yanzu haka suke samu a wajen kasashen Musulmi?

A ranar Asabar ne Farai Ministan Malaysia Najib Razak ya ce ‘yan kabilar Rohingya suna “fuskantar azabtarwa da fyade da kuma kisa.”

Ya ce abin kunya yadda gwamnatin Myanmar ta ki yin komai game da al’amarin.

Hakazalika, gwamnatin Pakistan ta ce ta kira jakadan Myanmar da ke kasar a wani mataki na “nuna rashin amincewa da farmakin da ake kai wa Musulmin Rohingya.”

RohingyaHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionZanga-zangar nuna goyon baya ga Musulmin Rohingya wacce kungiyoyin matan kasar Indonesiya suka yi a gaban ofishin jakadancin Myanmar da ke birnin Jakarta ranar Litinin

A makon jiya an rika samun jerin zanga-zanga a kasashen Indonesiya da kuma Indiya, inda ake Allah-wadai da gwamnatin Myanmar.

Sai dai sauran manyan kasashen Musulmi kamarsu Saudiyya da Masar da kuma Iran ba su ce komai ba tukuna.

Hukumomin kasar Bangladesh sun ce suna zargin dakarun gwamnatin Myanmar da binne nakiyoyi a kan hanyar da ‘yan gudun hijiran Rohingya ke bi, suna tserewa daga kasar.

Bangladesh ta kira jakadan Myanmar da ke kasar don nuna rashin jin dadinta. Sai dai gwamnatin Myanmar ta musanta aika ta hakan.

Mene ne gaskiyar hotunan da ake yada wa a kafafen sada zumunta?

Tun bayan fara rikicin ne na kwana-kwana nan ne ake samun labarai da hotuna da kuma bidiyo musamman a kafafen sada zumunta wadanda suke ikirarin nuna musgunawar da Musulmi ‘yan kabilar Rohingya ke fuksanta a Myanmar.

Sai dai galibin wadannan labaran da hotunan ba gaskiya ba ne.

Yawancinsu na wadansu rikice-rikice ne ko tashe-tashen hankula da suka faru a wani wuri a baya can, amma ba a Myanmar ba.

MyanmarHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionMisali wannan hoton ya fito ne daga kasar Bangladesh a shekarar 1971, amma sai aka rika wallafa shi a intanet a matsayin hoton kungiyar mayakan Rohingya
BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *