Nigeria: An sace fasinjoji a motar bas a Rivers

Idris KpotunHakkin mallakar hotoFACEBOOK

Matsalar sace mutane a yi garkuwa da su don neman kudin fansa ta dauki sabon salo a jihar Ribas da ke kudancin Najeriya, inda masu aikata wannan ta’asa suka shiga tarbe motocin haya, suna yin awon gaba da fasinjojinsu wadanda galibi masu karamin karfi ne.

Yanzu haka ma ana cike da damuwa game da wasu fasinjoji 19 da irin haka ta rutsa da su.

Sai dai rundunar ‘yan sandan jihar, ta ce a tsaye take wajen shawo kan matsalar, har ma ta kubutar da wasu daga cikin fasinjojin.

Al’amarin ya faru ne a ranar Alhamis kusa da garin Fatakwal, jim kadan bayan tashinsu daga tasha za su nufi garin Owerri na jihar Imo.

Amma a safiyar Juma’a jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar ta Ribas, Mista Omoni Nnamdi, ya ce sun yi azamar kai wa fasinjojin dauki.

“Kuma a wani tsararren kokari da aka yi, mun sami nasarar kubutar da 11 daga cikin fasinjojin. Ko da yake har yanzu wasu uku suna hannun ‘yan bindigar. Amma dai muna yin iya bakin kokarinmu don ganin an kubutar da su,” in ji Mista Omoni.

Ya kara da cewa, “Muna aiki tukuru, don ganin ba a sake samun aukuwar hakan ba. Mun kara yawan sintirin da mu kan yi da motoci a kan hanyar da al’amarin ya auku, kamar dai yadda muka yi a daya hanyar da aka rika samun irin wannan matsala, har aka kai ga samun sauki.”

Ya zuwa yanzu kuma rundunar ‘yan sandan jihar ta Ribas ta damke wasu daga cikin masu tafka wannan ta’asa, a cewar Mista Nnamdi.

“Suna taimaka mana da bayanai, hatta shugaban gungun masu aikata wannan ta’asa da muka kama, shi ma yana taimaka mana. Kuma muna nan muna kokarin fasa gayyar ‘yan bindigar,” in ji shi.

Sharhi daga AbdusSalam Ibrahim Ahmad

Da alamu matsalar tarbe motocin haya da ‘yan bindiga ke yi, su yi awon gaba da fasinjoji, tana neman zama wata babbar barazana a jihar Ribas.

A dan tsakanin nan dai ana ta samu aukuwar irin wannan matsala a jihar ta Ribas, al’amarin da Mista Omoni Nnamdi ya ce sun farga da hakan, kuma su ma sun yi wa matsalar kukan-kura:

Sace mutane don neman kudin fansa dai wata matsala ce da aka dade ana fama da ita a kudancin Najeriya, kuma ta kan shafi masu hannu da shuni ko masu rike da manyan mukaman gwamnati da iyalansu ne.

Amma yanzu abin yana nema ya zama kan mai tsautsayi, sakamakon yadda ya kan rutsa da hatta talaka dangin tsuntsu.

BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *