A bangare biyu kawai Buhari ya kware – Obasanjo

Tsohon Shugaban Najeriya Olusegun ObasanjoHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES

Tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya shaida wa BBC cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya yi kokari idan aka yi la’akari da yadda ya samu nasara a bangare biyu wadanda ya fi kwarewa a kai.

Mista Obasanjo ya ce Shugaba Buhari bai ba shi kunya ba saboda “al’amuran da muka san zai iya magancewa ya magance su.”

Ya ce shugaban ya fara magance matsalar cin hanci da rashawa da kuma yaki da masu tada kayar baya.

“Ba kowa ba ne zai gamsu da yadda yake yaki da cin hanci, amma abu muhimmi shi ne ya fara yaki da matsalar. Hakazalika mun san cewa a matsayinsa na tsohon soja zai yi iya kokarinsa wajen magance matsalar masu tada kayar baya,” in ji shi.

  • Guguwar Buhari ta zame mana matsala — Dalung
  • Atiku ya caccaki gwamnatin Buhari

Ya ci gaba da cewa ba zai taba yiwu ba a magance matsalar Boko Haram gaba daya, a tashi guda, “saboda manyan abubuwan da suka jawo ta kamar talauci da rashin aikin yi da jahilci har yanzu suna nan, ba a magance su ba,” kamar yadda ya ce.

An tambaye shi ko zai sake goyon bayan Shugaba Buhari idan ya sake tsayawa takara a zabe mai zuwa.

Sai ya ce: “Idan ya ce zai kara tsayawa takara zan duba aikin da ya yi duka, daga su ne zan yanke hukunci. Na zabe shi shekara biyu da suka wuce ne saboda zan iya zabar kowa amma fa ban da Goodluck Jonathan,” a cewar Mista Obasanjo.

BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *