Matsafa ne suka sa muka fadi zabe — Jacob Zuma

ZumaHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionZuma ya ce fatalwa ne suka zabi DA

Shugaban kasar Afirka ta kudu Jacob Zuma ya yi zargin cewa matsafa ne suka sa jam’iyyarsa ta kasa kayar da jam’iyyar hamayya ta Democratic Alliance (DA) a zaben Yammacin Cape inda suka fi karfi.

Jaridar the Sowetan Live ta ambato shi yana cewa, “A zabukan da suka gabata na gamsu cewa za mu lashe zaben Yammacin Cape‚ har sai da na fadi cewa za mu yi nasara.

Yanzu mene ne ya faru? Ban san irin amsar da zan bayar ba.

Ban sani ba, watakila matsafa ne suka yi kulle-kullensu.”

A wurin wani jawabi da ya yi magana da harsunan isiZulu da isiXhosa, jaridar ta kuma ambato Zuma yana cewa watakila fatalwa ne suka zabi DA.

“Ban san inda suka samu wannan sa’a ba saboda akasarin mutane ba su gamsu da jam’iyyar ba. Amma dai ina tsammani fatalwa ne suka yi zaben.”

Jaridar Sowetan Live ma ta ruwaito Mista Zuma yana cewa a halin yanzu ma matsafa “na amfani da lantarki”.

Ya yi wadannan kalaman ne jiya a yayin da yake jawabi a gaban mambobin jam’iyyarsu a garin Strand dake kudu maso gabashin kasar shekara guda bayan da jam’iyyar ta ANC ta sha wani babban kaye a zaben kananan hukumomi.

  • An kama Boka a kan satar mota a Kenya
  • Yadda aka kama masu cin naman mutane a Afirka Ta Kudu

Jam’iyyar ta Democratic Alliance ta kwace yankuna masu muhimmanci a shekarar 2016 wadanda suka hada da babban birnin kasar Pretoria.

Shugaba Zuma ya tuhumi ‘yan adawa da “amfani da kudi, da sayan kuri’un mutane”. Da alama yana magana ne a kan kokarin tumbuke shi sau takwas da aka yi a baya, yunkurin da ba su yi nasara ba.

Jaridar ta kuma ruwaito Mista Zuman na cewa ba zai bace ba ko da wasu sun sa masa guba.

“Ina tare da ku ko bayan wa’adin mulki na ya kare. Zan kasance a rassan bishiyoyi, ina magana”.

BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *