Ambaliya na dab da mamaye wasu sassan Jihar Kogi

AmbaliyaHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya NEMA, ta umarci wasu al’ummomin jihar Kogi da su bar garuruwansu saboda gudun ka da ambaliyar ruwa ta mamaye su.

NEMA ta ce garuruwan da ake tsammanin za su fuskanci ambaliyar sun hada da Sarkin Noma da Ganaja da ke karamar hukumar Lokoja da kuma karamar hukumar Igala mela da ma wasuu garuruwan da dama.

Hukumar NEMA ta ce tuni ta tuntubi kwamishinan kula da muhalli na jihar da hukumar agajin gaggawa ta Kogi da kuma sauran masu ruwa da tsaki kan yadda za a shawo kan lamarin.

Ta kuma kara da cewa an shirya wata tawaga da za ta je jihar don daukar matakan da suka dace a kan mutanen yankunan da ake sa ran abin zai shafa.

NEMA dai ta yi gargadi mai karfi ga mazauna yankunan da ambaliyar ke da yiwuwar afkawa da su koma wurare mafiya aminci don gudun wannan ambaliya da ka iya faruwa nan da ko wanne lokaci ta yi musu barna.

  • Beraye sun haddasa ambaliyar ruwa a India – Minista
  • Yadda ambaliya ta yi raga-raga da gidaje kusa da Abuja
  • Nigeria: ‘Jihohi 30 za su fuskanci ambaliyar ruwa’

Dama tun a watan Yuli ne mahukunta a Najeriyar suka yi gargadin cewa kusan jihohi 30 ne za su fuskanci bala`in ambaliyar ruwa a bana, sakamakon mamakon ruwan sama da ake tafkawa.

Masana sun bayyana cewa irin wannan ruwan saman alama ce ta tasirin sauyin yanayi ne a kan wasu kasashen Afrika, ciki har da Najeriya.

BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *