Isra’ila ta kori wasu Falasdinawa daga Gabashin Birnin Qudus

Ayoub Shamasneh (2nd right) and unidentified others outside the home in Sheikh JarrahHakkin mallakar hotoAFP
Image captionIyalin Shamasneh sun kwashe shekara da shekaru suna zaune a gidan

‘Yan sandan Israila sun kori wasu iyalai Falasdinawa daga gidansu da ke Gabashin birnin Qudus, wanda aka kwashe shekaru ana takaddama a kansa.

Iyalan Shamasneh sun fice daga gidan, wanda suka kwashe shekara 53 a cikinsa, bayan wasu kotunan Isra’ila sun yanke hukuncin cewa gidan mallakin Yahudawa ne.

Dokokin Isra’ila sun amincewa dan kasar ya sake mallakar fili ko gidan da ya rasa bayan Jordan ta mamaye Gabashin Qudus a yakin da aka yi a 1948-9.

Isra’ila ta mamaye yankin tun lokacin da ta fatattaki Jordan a 1967.

Ranar Talata da safe, an tura ‘yan sanda gundumar Sheikh Jarrah d a lokacin da jami’ai ke korar iyalin Shamasneh daga gidan.

Kafofin watsa labarai sun ce iyalin su shida, cikinsu har da mai shekara sama da tamanin, sun fice daga gidan suka tsaya a waje tare da masu fafautika.

A new occupant peers round the door of the newly vacated house (05/09/17)Hakkin mallakar hotoAFP
Image captionYahudawan da aka bai wa gidan sun koma cikinsa bayan an kori Falasdinawan.

“Wannan ba karamin cinzali ba ne,” in ji Fahamiya Shamasneh, mai shekara 75, a hirarsa da kamfanin dillancin labarai na AFP. “Watakila za mu rika yin bacci a kan titi.”

Jaridar Jerusalem Post ta ruwaito cewa daya daga cikin mutanen da aka kora ya yi yunkurin fasa saman gidan ya koma ciki amma jami’an tsaro sun hana shi, inda suka yi barazanar kama shi.

Yahudawan da aka bai wa gidan sun koma cikinsa bayan an kori Falasdinawan.

Israeli police and an ambulance at scene of eviction in Sheikh JarrahHakkin mallakar hotoAFP
Image caption‘Yan sandan Isra’ila sun toshe hanyar zuwa gidan kafin su kori mazauna cikinsa.
BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *