Hotunan abin da ya faru a Afirka makon jiya

People colourfully dressed at a festivalHakkin mallakar hotoEPA

Wani bikin al’adar kabilar Ebrie wadanda suke danganta kansu da Daular Ashanti a birnin Abidjan na kasar Kwaddibuwa.

Men dancingHakkin mallakar hotoEPA

Kimanin shekara 300 ke nan ana gudanar da wannnan bikin.

A woman sells clothes at a street market in CairoHakkin mallakar hotoREUTERS

Wata ‘yar kasuwa a wata kasuwar Tufafi da ke birnin Alkhahira a kasar Masar ranar Alhamis.

An Egyptian man holds a sheep ahead of the Eid al-Adha at a local marketHakkin mallakar hotoEPA

Wani mai sayar da dabbobi a wata kasuwar dabbobi gabanin bukukuwan babbar sallah a birnin Giza na kasar Masar.

A scavenger carries recyclable plastic materials packed in a sack at the Dandora dumping site on the outskirts of Nairobi, Kenya August 25, 2017. Picture taken August 25, 2017.Hakkin mallakar hotoREUTERS

Wani dan bola jari a wani babban wurin zubar da shara a birnin Nairobi na kasar Kenya gabanin haramta amfani da leda a kasar cikin makon jiya.

A model strikes a pose for the "A Nasty Boy Magazine"Hakkin mallakar hotoAFP

Wani mai tallan kayan kawa yayin da ake daukarsa hoto a birnin Legas na Najeriya.

PhotoshootHakkin mallakar hotoAFP

Masu tallan kayan kawan ana daukarsu hoto ne sanye da guntun siket don a wallafa a wata mujalla mai suna, A Nasty Boy Magazine, wadda fafutikar kawo daidaito tsakanin ‘yan mata da maza a fannin tallata jiki.

A rebel soldier posing with his weaponHakkin mallakar hotoREUTERS

Wani dan tawaye a garin Yondu kusa da birnin Kaya na kasar Sudan ta Kudu.

Rebel soldiersHakkin mallakar hotoREUTERS

‘Yan tawayen suna shirin kai wa wani sansanin dakarun gwamnatin Sudan ta Kudu hari ne a birnin Kaya kusa da iyakar kasar da Uganda.

A migrant, who was not allowed to return to her country with other migrants for not having complete documents, cries as she is comforted at a detention center inTripoli, Libya, August 29, 2017.Hakkin mallakar hotoREUTERS

Wata ‘yar ci-rani tana bai wa ‘yar uwarta hakuri saboda ita ba ta samu kubuta daga wata cibiyar tsare su a birnin Tripoli na kasar Libya ba, a ranar Talata.

Supporters celebrate in a street of Dakar after the courthouse has decided to release activist Kemi Seba from the Rebeuss jailhouse on August 29, 2017. Kemi Seba was arrested after he burned a 5,000 CFA franc bank note during a meeting on August 19, 2017.Hakkin mallakar hotoAFP

Wadansu masu goyon bayan wani mai fafutika, Kemi Seba, yayin da suke murnar sakinsa a birnin Dakar na Senegal ranar Talata.

Libyans dressed up in traditional costumes ride horses during a race in Tripoli, Libya, August 19, 2017. Picture taken August 19, 2017.Hakkin mallakar hotoREUTERS

Wadansu ‘yan kasar Libya lokacin da suke wasan tseren dawakai a babban birnin kasar Tripoli ranar Asabar din makon jiya.

Hotuna daga AFP, EPA, Getty Images da kuma Reuters

BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *