‘Yan wasan Nigeria Super Eagles sun isa Cameroon

'Yan wasan NajeriyaHakkin mallakar hotoNFF
Image captionSuper Eagles sun taka rawar gani sosai a karawar farko ranar Juma’a

‘Yan wasan Super Eagles na Najeriya sun isa birnin Yaounde gabanin sake karawarsu da Kamaru ranar Litinin a wasan share fagen zuwa gasar cin Kofin Duniya wacce za a yi badi a Rasha.

A ranar Juma’a ne kasashen biyu suka yi fafatawar farko a filin wasa na Godswill Akpabio da ke jihar Akwa Ibom a Najeriya, inda Kamaru ta yi rashin nasara da ci 4-0.

Najeriya ce kan gaba a rukunin B, inda take da maki tara.

Zambia ce ke biye mata da maki hudu sai Kamaru mai maki biyu.

Aljeriya ce kurar baya inda ta ke da maki daya kacal bayan wasa uku.

‘Yan wasan Super Eagles na fatan sake samun nasara a wasan na ranar Litinin domin sake karfafa matsayinsu a saman teburin rukunin na B.

Kasar da ta zo ta daya ce kawai za ta samu damar zuwa gasar ta duniya, wacce Rasha za ta karbi bakunci a badi.

Otel din da 'yan wasan Super Eagles suka sauka a birnin YaoundeHakkin mallakar hotoNFF
Image captionOtel din da ‘yan wasan Super Eagles suka sauka a birnin Yaounde

BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *