‘Chelsea za ta maka Costa a kotu’

Diego CostaHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionCosta ya koma Chelsea daga Atletico Madrid a shekarar 2014

Wadansu majiyoyi na kusa da dan kwallon Chelsea, Diego Costa, sun ce yana shirin koma wa kulob din don ya kara gwada sana’arsa ko za a ba shi damar taka leda, in ji Telegraph.

Jaridar Express ta ruwaito cewa Chelsea ta shirya kai dan wasan kara a gaban kotu, inda za ta bukaci dan kwallon ya biyata tarar fam miliyan 50 idan bai dawo kulob din ba.

Kungiyar Real Madrid ta yi shirin maye gurbin Cristiano Ronaldo da Kylian Mbappe kafin rufe kasuwar saye da sayar da ‘yan wasan Turai, amma sai hakan bai yiwu ba saboda rashin amincewar kungiyar Monaco, in ji jaridar Sunday Times.

Dan wasa Cristiano RonaldoHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionA watan Yuni ne BBC ta ruwaito cewa Ronaldo yana son barin Spain saboda zargin da ake masa na zambar haraji

Hakazalika Madrid ta ki amincewa ta sayi dan wasan Arsenal Alexis Sanchez, amma za ta sake waiwayar batun sayensa a badi lokacin da yarjejeniyarsa ta kare da kulob dinsa, kamar yadda jaridar Express ta wallafa.

Kocin Liverpool Jurgen Klopp zai gana da Philippe Coutinho a mako mai zuwa bayan yunkurin dan wasan na komawa Barcelona ya ci tura, a cewar jaridar Star.

Jaridar Mirror ta ce Coutinho yana cikin fushi ganin yadda har yanzu bai samu tabbacin komawa Barcelonan a kaka mai zuwa ba.

  • ‘Tsada ce ta hana Barcelona sayen Coutinho’
  • Rooney zai gurfana a gaban kotu
  • Chelsea ta sayi Drinkwater

Ana ganin komawar Kylian Hazard kungiyar Chelsea za ta sa dan uwansa Eden Hazard ya sabunta yarjejeniyarsa da kungiyar, kamar yadda jaridar Express ta bayyana.

Daraktan Barcelona Robert Fernandez ya ce sun so su sayi dan kwallon Paris St-Germain (PSG) Marco Verratti a kakar bana, in ji jaridar Mail.

Jaridar Mirror ta ruwaito cewa Barcelona ta kasa mallakar tsohon dan wasan Manchester United Angel di Maria ne, bayan da PSG ta bukaci ta biya fam miliyan 64.

BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *