Tsawa ta fada wa mutane 15 a Faransa a bikin kade-kade

Hoton wata tsawa a FaransaHakkin mallakar hotoAFP
Image captionAna gargadin jama’a a sassa da dama na Faransa kan hadarin faduwar mummunar tsawa

Tsawa ta raunata mutane akalla 15, biyu daga cikinsu abin ya yi tsanani, a wani wurin bikin kade-kade da wake-wake a arewa maso gabashin Faransa, kamar yadda hukumomi suka ce.

Tsawar ta fadi a wurare da yawa a wurin bikin na Vieux Canal a garin Azerailles, kamar yadda hukumomin suka ce.

Daga cikin wadanda suka samu kunar har da wasu yara da suke cikin wani tanti a lokacin.

Wata mata mai shekara kusan 60 da kuma wani mutum mai kimanin shekara 40 sun jikkata sosai a lamarin.

Galibi a irin wannan lokaci na shekara akan gargadi jama’a a kan hadarin yawan faduwar tsawa mai tsanani a sassan kasar Faransar.

Bayan lamarin an dage dukkanin bukukuwan na ranar Asabar, wanda daga cikin mawakan da za su sheke aya akwai Pony Pony Run Run na Faransa da kuma Black Bones.

BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *