Tsohon dan wasan Hausa, Kasimu Yero ya rasu

Marigayi Kasimu YeroHakkin mallakar hotoWHATAPPS
Image captionKasimu Yero ya fi yin fice a fagen wasan barkwanci

Tsohon shahararren dan wasan kwaikwayon Hausa, Kasimu Yero ya rasu, kamar yadda wani na kusa da marigayin ya shaida wa BBC.

Marigayin ya rasu ne ranar Lahadi a garin Kaduna a arewacin Najeriya bayan doguwar jinya.

Ya yi fice ne a shekarun 1980 lokacin da yake fitowa a shirye -shiryen kafar yada labarai ta kasar wato NTA – a wasannin Magana Jari Ce (na Hausa da na Turanci) da Karanbana da dai sauransu.

  • ‘Yan fim na zubar mana da mutunci — Bosho
  • Yin fim ya fi aikin gwamnati — Hafsa Idris

Ana ci gaba da mika sakon ta’aziyya game da rasuwar dan wasan wanda ya shahara wajen barkwanci.

Jarumin fina-finan Hausa, Ali Nuhu ya yi fatan Allah Ya jikan marigayin, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Instagram.

BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *