Awamiya: ‘Saudiyya ba ta yarda da adawa daga ‘yan shi’ar kasar’

Remains of a car and buildings in the town of Awamiya, Saudi Arabia (9 August 2017)Hakkin mallakar hotoREUTERS/FAISAL AL NASSER

Wakiliyar BBC Sally Nabil ta samu izinin da ba kasafai ake samu ba na shiga Awamiya a kasar Saudiyya, wani gari da ya gigice a watannin baya-bayan nan saboda munanan artabu tsakanin dakarun tsaro da ‘yan ta-da-kayar-baya mabiya shi’a sakamakon rushe tsohon yankinsa a gabashin masarautar da musulmi ‘yan Sunni ke mulki.

“Za mu ba ku ‘yan mintuna kalilan ne kawai. Idan muka ce ‘tafi’, to, ku wuce nan take,” wani jami’in dan sanda ya fada mana lokacin da muka hau wata motar sulke zuwa Awamiya.

Yayin da muka tunkari garin, cikin rakiyar zaratan dakaru, jami’an sun yi ta zantawa da kwamandojinsu ta wayar tarho don tabbatar da cewa ayarin na cikin amincin da zai iya ci gaba.

Sha’anin tsaro a Awamiya har yanzu bai daidaita ba, ko da yake, gwamnati ta ce ta shawo kan komai.

Saudi special forces member holds patrols the town of Awamiya (9 August 2017)Hakkin mallakar hotoREUTERS/FAISAL AL NASSER
Image captionThe Saudi interior ministry has blamed the unrest on “terrorist groups”

Mene ne tarihin birnin Awamiya?

Al-Awamiyah, wani kauye ne da ke tsakanin yankin Al-Qatif cikin Lardin Gabashin Saudiyya. Ya zuwa shekara ta 2009, yana da jama’ar da ta kai yawan mutum 25,500.

Al-Awamiyah ya yi iyaka da gonakin Al-Ramis a gabas da wasu gonakin a yammaci da kudancinsa.

A bangaren arewa, akwai iyakar da ta raba Al-Awamiyah da birnin Safwa mai makwabtaka, ta yadda garin ba zai iya ci gaba da fadada ba ko kadan, don samar da gidaje ga jama’arsa da ke bunkasa.

Saboda wannan kaidi, mutane na fita daga garin inda suke zuwa yankunan da ke kusa suna yin matsugunnai, mafi suna cikinsu shi ne Al-Nasera wanda ke da yawan mutane kusan 2, 500 da ke rayuwa a gida 250.

Awamiya ya kuma yi kama da irin garuruwan da ke fama da yaki, sakamakon yawan fadace-fadace da zanga-zanga.

Tattalin arziki

Tattalin arzikin Al-Awamiyah akasari ya dogara ne kan ayyukan hakar man fetur da noma.

Noma

Garin takanas ya shahara kuma ya yi fice da tumatirinsa wanda ake kira tumatur dan Ramsi, ya ci sunan kasar da ake nomansa wato Al Ramis.

Man fetur

Butatan man fetur sun zagaye garin daga yamma da arewacinsa har ma da rijiyoyin mai da dama wadanda wasunsu sun tsufa wasu kuma sabbin hakawa ne a wani bangare na aikin bunkasa Qatif.

Fiye da ganga miliyan biyu ta man fetur ce ke wucewa ta wannan gari kullu yaumin a kan hanyarsa ta zuwa tashar ajiya da matatar mai ta Ras Tanura.

Sufuri

Filin jirgin sama

Garin na amfani da Filin Jirgin Saman Kasashen Duniya na Sarki Fahd da ke kusa, tafiyar minti 25 ce za ta kai ka tazarar kilomita 30 daga tashar saukar matafiya zuwa garin.

Babban titi

Ana iya shiga garin ta ko wacce fuskar Babban titin Dhahran zuwa Jubail; wato hanyar fitowa daga Filin Jirgin sama ko kuma ta hanyar babbar kofar Qatif a kusa da Awjam.

Addini

Kusan duk mazauna garin Awamiyah mabiya tafarkin Shi’ah Imamiyya ne. Duk da azabtarwar gwamnatin Saudiyya, mazauna garin na kokarin yin bukukuwa da tunawa da muhimman ranakun mabiya darikar Shi’ah.

Fitattun mutanen da suka fito daga Awamiyah

Gwamnatin Saudiyya ta zartar wa Babban malami Nimr al-Nimr hukuncin kisa ranar 2 ga watan Janairun 2016 saboda kiraye-kirayensa na a kawo sauyin dimokradiyya.

Ana kwarzanta shi ta hanyar rubuta sunansa a jikin ganuwar garin da kuma sanya hotunansa a jikin allunan tallace-tallace har ma da zauruka kusa da na Imam Husayn ibn Ali.

Shi ma dan dan’uwansa, Ali Mohammed Al Nimr, yana fuskantar hukuncin kisa saboda ire-iren wadannan zarge-zarge.

Yawan ‘yan Shi’a a Awamiya

Hukumomi sun ce tsofaffin gine-gine suke rushewaHakkin mallakar hotoREUTERS/FAISAL AL NASSER
Image captionHukumomi sun ce tsofaffin gine-gine suke rushewa

Shiga Awamiya

Da muka shiga Awamiya, girman barnar da aka yi na da firgitarwa. Garin ya fi kama da fagen yaki – tamkar muna Mosul ko Aleppo.

Garin, wanda ke cikin yankin Qatif mai arzikin man fetur a Lardin Gabashi, na tsugunnar da mutane kimanin 30,000, akasarinsu ‘yan Shi’ah.

Yanzu, babu wani abu da ya rage na gine-ginensa masu tumbatsa illa gidajen da aka yi wa ruwan harsasai, da motoci da shagunan da suka kone kurmus – wannan wani tambari ne na gagarumin fada.

Tsawon shekaru, tsirarun mabiya darikar Shi’ah a Saudiyya na korafi kan abin da suke gani a matsayin nuna bambanci da ture su gefe a hannun sarakunan Sunni.

Sai dai bijirewarsu a ko da yaushe kan fuskanci murkushewa.

“Gwamnatin Saudiyya ba ta yarda da adawa ba, ko daga dan Sunni ko daga dan Shi’ah ce. Su dai kawai suna da gajen hakuri,” Ali Adubisi, daraktan kungiyar kare Hakkin Dan’adam ta Saudiyya mai sansani a Berlin ya fada mini.

Da na zagaya cikin garin Awamiya, Na ga motocin buldoza kalilan da ke tsaye cikin tsakiyar shara.

A watan Mayu, hukumomi sun fara rushe unguwar Musawara mai tsawon shekara 400, a wani yunkuri na abin da suka kira “aikin raya kasa”.

“An rushe gida 80, kuma har yanzu akwai gidaje kimanin 400 da suka rage. Gidaje ne da sun tsufa, ya kamata a zamanantar da su,” mai rikon mukamin magajin gari Essam Abdullatif Al-Mulla ya fada mini.

“An sauya wa iyalan matsugunnai bayan an biya su gwaggwabar diyya da yi musu tayin sauyin gidaje.”

Map of Saudi Arabia

Da zarar an fara rushe-rushen, sai dambarwa a Awamiya ta koma zuwa tarzoma.

Kungiyoyin Shi’ah sun zargi ‘yan sanda da tursasawa mutane barin garin, da nufin murkushe masu bijirewa.

Masu fafutuka sun ce dakarun tsarun sun garkame kofofin garin a watan Yuli, inda suka hana mazaunan da suka rage damar samun ayyukan tilas na rayuwa irinsu kula da lafiya.

Kungiyoyin Shia na sukar Saudiyya da cewa suna tursasawa dubban mutane barin AwamiyaHakkin mallakar hotoREUTERS/FAISAL AL NASSER
Image captionKungiyoyin Shia na sukar Saudiyya da cewa suna tursasawa dubban mutane barin Awamiya

Tarzoma ta yi sanadin mutuwar fiye da farar hula 20, a cikinsu har da wani yaro dan shekara uku da ya rasu a makon da ya gabata, baya ga karin ‘yan ta-da-kayar-baya akalla biyar, a cewar ‘yan fafutuka.

Hukumomin Saudiyya sun ce dan sanda takwas da dakaren tsaro na musammam hudu sun mutu, amma ba su ba da wani bayani game da mace-macen fararen hula da ‘yan ta-da-kayar-baya ba.

Ma’aikatar harkokin cikin gida ta dora alhakin rikicin a kan “kungiyoyin ‘yan ta’adda da suka dade cikin yankin tsawon shekaru”.

Wata sanarwa ta ce an sha kai wa dakarun gwamnati farmaki da gurnetin da ake harbawa da roka da bam din fetur da kuma bindigogin mashinga.

“‘Yan ta’adda ba-ji-ba-gani sun kashe fararen hulan, da suke labewa a cikinsu. Mutane sun tsere saboda barazanar ‘yan ta-da-kayar-baya,” ta kara da cewa.

Wani masallaci da aka rushe sakamakon rikici a AwamiyaHakkin mallakar hotoREUTERS/FAISAL AL NASSER
Image captionMasu fafutuka sun ce rikicin ya yi sanadin mutuwar fararen hula 20

Sai dai akwai daya bangaren na wannan bayani.

Na yi kokarin gano wani mutumin Saudiyya wanda ya tsere daga garin Awamiya, kuma a yanzu yake neman mafaka a Jamus.

“Dakarun tsaro kan harbi kowa – namiji ko mace ko dattijo kai har yaro ma,” a cewarsa.

“Tsawon kwanaki na kasa fita ko kofar gidana. Saboda tsananin tsoro.”

Mutumin, wanda ya bukaci kada mu bayyana sunansa don yana fargaba kan abin da zai same shi, ya fada mini cewa shi a karan kansa bai taba daukar makamai ba amma ya fahimci dalilin da ke sanya wasu yin haka.

“Ana iya yanke ma hukuncin kisa a Saudiyya kawai saboda kai dan Shi’ah ne don haka kana wani addini na daban.”

“An takure jama’a, an hana su ‘yanci kuma ba martabawa, kai ana ma iya zartar ma hukuncin kisa a wata shari’ah maras adalci. Ba za su iya yin shiru har abada ba. Idan wani ya harbe ka, dole kai ma ka rama.”

Masu fafutuka sun ce dakarun tsaro sun rufe hanyoyin shiga da fita daga birnin a watan YuliHakkin mallakar hotoREUTERS/FAISAL AL NASSER
Image captionMasu fafutuka sun ce dakarun tsaro sun rufe hanyoyin shiga da fita daga birnin a watan Yuli

Mutumin ya tuna farkon fara zanga-zangar ‘yan Shi’ah a Awamiya cikin shekara ta 2011, lokacin da Juyin-juya-halin Kasashen Larabawa ya zaburas da su har suka auka kan tituna.

“Mu masu zanga-zangar lumana ne, amma sai dakarun tsaro suka yi amfani da harsasan bindiga wajen tarwatsa mu,” in ji shi.

Tun daga nan ne, aka yi ta kama daruruwan mutane.

Kungiyoyin Kare Hakkin Dan’adam sun ce kotunan manyan laifuka da aka kafa don kararrakin ta’addanci, sun yanke wa mutane sama da 30 ciki har da yara hukuncin kisa bayan sun same su da laifukan da ke da alaka da zanga-zanga sakamakon shari’o’i marasa adalci.

Masu fafutuka na fargabar cewa masu zanga-zanga guda 14 ciki har da mutum hudu da aka same su da laifukan da suka aikata lokacin yarinta, ka iya fuskantar zartar musu da haddi a kowanne lokaci.

Mutanen sun hadar da dan baffan Sheikh Nimr Baqir al-Nimr, fitaccen malamin Shi’ah mai kaifin harshe wajen sukar gwamnati wanda aka tuhume shi da laifukan ta’addanci kuma aka zartar masa da hukuncin kisa a watan Janairun 2016.

Wani hoto na jagoran Shi'a a Awamiya Sheikh Nimr al-NimrHakkin mallakar hotoREUTERS/FAISAL AL NASSER
Image captionHar yanzu ‘yan garin Awamiya na sanya hoton jagoran Shi’a na Saudiyya Sheikh Nimr al-Nimr a jikin gine-gine

Harbe-harben bindigogi da muka ji na tashi daga nesa, sun katse mana gajeriyar ziyarar da muka kai garin Awamiya.

Ba mu da masaniya ko ‘yan sanda ne, ko kuma kungiyoyi masu gwagwarmaya da makamai ne, Mu dai ala dole nan take mu tafi, kamar yadda kwamanda ya ce.

A kan hanyarmu ta dawowa, Na duba ta gilashin tagar mota, ina mamaki anya rayuwa za ta iya komawa daidai cikin wani lokaci kusa a wannan gari da ya yi kaca-kaca.

Abu ne mai wahala a iya cewa ga lokacin, don kuwa dalilan da suka janyo rikice-rikicen har yanzu suna nan.

BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *