Boko Haram: Birtaniya ta rage agajin da take bai wa Nigeria

Priti PatelHakkin mallakar hotoREUTERS
Image captionPriti Patel ita ce mai kula da tallafin da Birtaniya ke bai wa kasashen waje

Birtaniya za ta rage yawan kuɗaden da take bai wa Najeriya a matsayin agaji domin ayyukan jin kai nan da ‘yan shekaru masu zuwa.

A shekarar 2016 Birtaniya ta kashe fam miliyan 100 wurin tallafawa ayyukan jin kai a Najeriya.

Amma a cikin shekara hudu masu zuwa ta yi alkawarin fam miliyan 200 kadai. Fam miliyan 50 ke nan a kowace shekara.

Ana san ran za a yi amfani da kuɗaden wurin tallafawa wadanda hare-haren Boko Haram ya shafa a arewa maso gabashin kasar.

A wata ziyarar kwanaki biyu da Sakataren Harkokin ci gaban kasashen waje ta kasar, Priti Patel ta kai Najeriya, ta nemi hukumomin kasar su kara daukar matakai na yakar masu tsattsauran ra’ayi.

Ta kara da cewa kamata ya yi wasu ƙasashe waje su taimaka wajen ba da tallafi.

Hare-haren kungiyar Boko Haram sun yi sanadiyyar raba mutum miliyan 1.5 daga muhallansu.

Hakan kuma ya shafi harkar noma a kasar wanda ke haifar da matsalar karancin abinci mai gina jiki.

BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *