Gwamnati za ta kashe fiye da Dala biliyan biyar kan aikin wutar Mambila

Gwamnati za ta kashe fiye da Dala biliyan biyar kan aikin wutar Mambila

Gwamnatin Tarayya ta amince da kwantiragin madatsar wuta ta Mambila kan Dala biliyan biyar da digo 792.
Kwantiragin ya hada da aiki gine-gine da hada na’urorin samar da wutar kuma da zarar an kammala aikin zai samar da wuta mai karfin fiye da megawat dubu uku kwatankwacin kusan rabin daukacin karfin wutar da ake samarwa a kasar baki daya.
Ministan Wuta da Ayyuka da Gidaje, Babatunde Raji Fashola ya fada wa manema labarai a fadar shugaban kasa jim kadan bayan majalisar kasar ta amince da kwantiragin jiya.
“Najeriya ta fara batun aikin tun shekarar 1972 wato kimanin shekaru 45 da suka gabata. An yi ta yi kokari don a gudanar da aiki amma ina mai farin cikin bayyana cewa wannan gwamnati ta amince da kwantiragin ga kamfanin kasar China kan Dala biliyan biyar da digo 792 kuma za a kwashe kimanin shekaru shida ana yi”. Inji shi.
Aminiya

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *