Dangote ya sayar da hannun jari mai yawa

Image captionAliko Dangote ya dade yana shiga cikin jerin attajiran dduniya da Forbes ke wallafawa

Rukunin Kamfanonin Dangote ya sayar da hannun jari na miliyoyin daloli a kamfaninsa na siminti ga wasu masu zuba jari na kasashen waje a wani ciniki da ka iya juya akalar kasuwar hadahadar hannayen jari ta Najeriya.

A ranar Talata Dangote Industries, wanda mutumin da ya fi kowa wadata a Afirka Aliko Dangote ya mallaka, ya sayar da hannun jari miliyan 416 na Dangote Cement a kan kudi naira biliyan 86, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 236.

Malam Abubakar Aliyu, wani masanin tattalin arziki kuma daya daga cikin masu ruwa-da-tsaki a harkar saye da sayar da hannayen jari a Najeriya, ya shaida wa BBC cewa, “Wannan zai iya sa farashin hannun jarin kamfanin ya kara daraja, kuma abin da muke so ke nan a kasuwar hadahadar hannayen jari don hakan zai sa abubuwa su kara habaka”.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato wata majiya a kasuwar hadahadar hannayen jarin ta Najeriya tana cewa da ma kamfanin na Dangote Cement, wanda shi ne kamfanin simintin da ya fi girma a Afirka, yana sayar da hannayen jarinsa kadan-kadan don kara yawan jarinsa da ake saye da sayarwa a kasuwar.

  • Arzikin Aliko Dangote ‘ya ragu’
  • Dangote ya sasanta tsakanin Hausawa da Yarbawa

Sai dai kuma har yanzu babu wani bayani game da masu zuba jarin da suka sayi hannayen jarin na Dangote Cement.

Wasu majiyoyi a kasuwar dai sun ce mai yiwuwa wannan ciniki wani bangare ne na yunkurin da uwar kamfanin na Dangote ke yi na samar da kudi don ci gaba da aikin ginin matatar mai a Legas, aikin da ke fuskantar barazana sakamakon karancin kudi.

Sai dai Malam Abubakar Aliyu ya ce babu alamun kamfanin na Dangote na fuskantar matsala a kasuwar.

A makon jiya ne dai mujallar Forbes ta bayyana cewa arzikin shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya ragu sakamakon karayar da darajar naira.

Sayar da hannun jari mai yawa haka sakamakon wata matsala dai ka iya haddasa rudani a kasuwar, kasancewar Dangote na cikin kamfanonin da suka fi karfi a cikin wadanda ake hadahadar hannayen jarinsu a kasuwar.

BBC Hausa

Hassan Usman Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *